AKWAI ABIN TAUSAYI, DAURE KA KARANTA KAYI SHARE.
Wannan labarin wani yaro ne mai kimanin shekara 5 Mahaifiyarsa ta Rasu, sai yaga kawai ya dai na ganinta sai ya tambayi babanshi yace: Baba ina mama taje?,
se Baban yace: maman ka tana lahira, se Yaro yace: yaushe zata dawo? sai baban yayi shiru bai ce komai ba.
Wata rana yaron yana wasa da abokanshi, bayan angama wasa se kowa yace bari yaje gida gurin maman shi se yaron yace shima so yake idan ya girma ya samu kudi yaje Lahira don baban shi yace maman sa tana lahira, se daya daga cikin Abokansa yace: nima zaka je dani? sai yaron yace Ehh.
Wata rana yaron yana makarantar islamiyya malamin su yana wa'azi yana cewa 'duk wanda ya mutu idan yaje lahira bazai dawo ba' se yaron ya daga hannu yace malam to idan mutun be dawo ba toh me yakeyi acan?.
Sai malamin yace: Lahira gurine inda ake hisabi ga matattu kuma duk wanda ya mutu baya dawowa, Sai yaron yace: idan mutun ya mutu ina ake kaishi, sai malam yace makabarta, sai yaron yace: miyene mutuwa? sai malamin yace: mutuwa tana nufin fitar Ruhi daga jikin dan Adam, sai yaro yace: Toh ina Ruhi yake ajikin dan
Adam? sai malam yace kai yaro ka cika tambaya dayawa, Je ka zauna.
Washe gari bayan sallar Asuba sai yaron yazo gurin babanshi yace ina kwana baba ka tashi lafiya? Baban yace lafiya kalau, sai yaron yace baba Ina da tambaya, sai yace to ina jinka É—ana miye Tambayarka? Se yaron yace: baba wai ina Ruhin mamana yake? sai baban yayi shiru............. Can sai baban yace: Yaro saurara in baka wani labari mamanka ta Rasu, Rasuwa kuma idan akayita ba'a dawowa duk wanda aka zarewa Ruhi daga jikinsa bazai rayu ba, lokacin mamanka ne Yayi Shi Yasa Ta rasu, nima idan lokaci na yayi zan mutu na Barka.
Sai yaron yace: toh baba don ALLAH idan zaka mutu ka gayamin domin nima inaso na mutu se In raka ka zuwa gurin mamana naji kewarta wlh Baba, sai baban yayi shiru don yaga alamar yaron nan yana son maman sa kuma yaga alamar lallai yaron yana buƙatar ganin maman shi, sai baban shi yace je ka shirya kazo muje zan kaika inda maman ka take yanzu.
Sai yaro yaje yayi wanka yaci kwalliya yana murna zaije gurin maman sa da sauri yazo gurin Babanshi yace Baba gani na shirya muje, sai Baban ya kama jannun yaron suka fita suna ta tafiya har suka bar gari suka shiga daji, suka Isa makabarta, sai Baban ya nufi ƙabarin maman wannan yaron.
Sai Baban yace; yaro maman ka tana cikin wannan ƙasar, wannan ƙasar itace ƙabari, kuma duk wanda ya mutu a ciki ake saka shi, kuma duk wanda ya mutu baya iya motsi baya iya komai, a haka za'a kawoshi
anan gurin kuma a binneshi baya iya yin komai sai ikon ALLAH, sai yaro ya fashe da kuka ya faɗi ƙasa yace: Mamana yanzu itace a cikin wannan ƙasa?
Sai yace toh Baba wani laifi tayi da ALLAH ya kashe ta? Sai Baban yace kowa haka ze mutu idan lokaci yayi, suna zaune sai ga wasu mutane sunzo da gawa za'a binneta a cikin ƙabari sai yaron ya ƙura ido yaga duk yanda ake binne mutun, sai suka dawo gida, da suka dawo gida a duk lokacin da yaron yayi sallah sai yace ALLAH ka jiƙan Mamana!
Yaron ya tara kuÉ—in wasa, irin takardun da yara ke kira kuÉ—i yakai wa malamin su yace malam na baka wannan kuÉ—i ne don kayiwa mamana Addua! Malam yayi shiru yana jin tausayin wannan yaron yace kabar kuÉ—in ka zan yiwa mamanka Addua kyauta, yaro cikin kuka yace Nagode!
Yaro Dan ƙarami kenan, wanda bai mallaki hankalin shi ba! Ina ga kai kuma dake da Hankali?
.
Ya Allah ka jiƙan Iyayenmu, ka gafarta musu zunubansu, ka sanya Aljannna itace makomarsu!
Don girman Allah É—an uwa idan ka karanta kayi sharing saboda al'umma su Amfana da kai.

0 Comments