Yar takarar kujerar gwaman jihar Adamawa ƙarƙashin jam'iyyar APC Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na bayyana zaɓen gwaman jihar a matsayin wanda bai kammala ba
Yayin da ta bayyana a cikin shirin 'Politics Today' na gidan talbijin ɗin Channels Tv, Sanata Aishatu Binani ta yi maraba da matakin, inda ta yi zargin cewa an aikata kura-kurai da rikice-rikice a wasu ƙananan hukumomin jihar.

0 Comments