Ticker

10/recent/ticker-posts

Bazanyiwa Sabon Gwamna Kasalandan Ba Inji Kwankwaso..Ga Cikakken Bayanin 👇

 Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Yace Bazai Yiwa Sabon Gwamna Kasalandan Ba A Ayyukansa.


Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen da ya wuce a Najeriya, Engr. Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai yi wa gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, katsalandan cikin harkokin mulkinsa ba.

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP na ƙasa, kuma wanda ake gani a matsayin ubangidan Abba Gida-Gida a siyasance, ya ce idan gwamnan mai jiran gado ya nemi shawararsa, zai ba shi.
Wasu mutane sun yi ta nuna fargabar cewa ba lallai ne Abba Kabir Yusuf ya samu cikakken ikon tafiyar da gwamnatin Kano ba, idan an rantsar da shi, saboda mai yiwuwa Kwankwaso zai yi ta ba shi umarni da yi masa katsalandan.

Sai dai, yaayin wata hira da BBC, tsohon gwamnan na Kano, ya ce a matsayinsa na ɗan Kano zai riƙa ankarar da gwamnatin wadda za a rantsar a ƙarshen watan Mayu, duk lokacin da ya ga ta kauce hanya.


Post a Comment

0 Comments