Al Hilal ta Saudiyya ta yi wa Messi tayin albashin da ya fi na kowa a duniya.
Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya, ta yi wa Messi tayin biyan sa albashin da ya fi na kowanne ɗan ƙwallo a faɗin duniya. (Mirror)To amma, ƙungiyar Inter Miami a Amurka na sa ran sayen zakaran ɗan wasan na duniya da kuma Sergio Busquets na Barcelona a kaka mai zuwa. (Sport - in Spanish)
Chelsea ta yi wa ɗan wasanta na tsakiya, Mason Mount farashin fam miliyan 70 duk da cewa ɗan Ingilan yana cikin shekarar ƙarshe ta kwanturaginsa a kulob ɗin. (Athletic)
Shi dai Mount yana sha'awar tafiya Bayern Munich ne, domin ya sake haɗuwa da tsohon kocinsa a Chelsea Thomas Tuchel. (Guardian)


0 Comments