Ticker

10/recent/ticker-posts

Mecece Gwamnatin Riƙon Ƙwarya Da Akeson Kafawa.. Ga Cikakken Bayanin 👇

 

A ranar Laraba ne hukumar ƴan sandan ciki ta Najeriya ta tabbatar da rade-radin da ake yi cewar akwai wata ƙullaliya ta ganin an kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya a ƙasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunanya ya sanya wa hannu ta ce “wani yunƙuri ne na jingine tsarin mulki da yin zagon ƙasa ga mulkin farar hula da kuma yunƙurin jefa ƙasar cikin rudani.

Sanarwar ta ƙara da cewa “masu kitsa lamarin sun tattauna kan hanyoyi da dama na aiwatar da shirin nasu, kamar haddasa mummunar zanga-zanga a manyan biranen Najeriya, wadda za ta haifar da kakaba dokar-ta-baci.

Ko kuma ta hanyar nemo izinin kotu domin dakatar da rantsar da sabuwar gwamnati da majalisar dokokin tarayya, ta hanyar da ba ta dace ba.

Ma'anar gwamnatin riƙon-ƙwarya


Gwamnatin riƙon-ƙwarya na nufin gwamnatin wucin-gadi ko kuma gwamnatin da ake kafawa na wani ɗan lokaci.

Wasu kuma kan kira ta gwamnatin miƙa mulki.

Ana kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ne domin ta yi aiki kafin samar da zaɓaɓɓiyar gwamnati mai zuwa.

A mafi yawan lokuta babban aikinta shi ne tsara harkokin siyasa da kuma yadda za a yi zaɓe domin samar da sabuwar gwamnati.

Manyan masu riƙe da lamurran ƙasa ne ke zaɓen waɗanda za su jagoranci irin wannan gwamnati, mafi yawan lokuta a lokacin da aka kawo ƙarshen wani yaƙin basasa.

Haka kuma, ana kafa irin wannan gwamnati a duk lokacin da aka soke zaɓe a ƙasa mai bin tafarkin dimokraɗiyya, bayan cikar wa’adin gwamnati mai ci.

A Najeriya an kafa gwamnatin rikon kwarya ta karshe ne shekaru 30 da suka gabata, a 1993, lokacin da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta soke zaɓen da aka gudanar, wanda ake yi wa laƙabi da June 12.





Post a Comment

0 Comments