Ticker

10/recent/ticker-posts

Jami,an Fasa Kwauri Sun Kama Kwantena 27 a Jihar Rivers..Ga Cikakken Bayanin 👇

 Jami'an hukumar hana fasa-Æ™wauri ta Najeriya reshen jihar River a kudu maso kudancin Najeriya sun kama wasu Kwantena 27 kan zargin saÉ“a Æ™a'ida wajen shigar da su cikin Æ™asar.

Babban jami'in hukumar mai kula da shiyyar jihar Baba Imam ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a garin Onne na jihar Rivers.

Imam ya ce an kama kwantenonin ne bisa laifukan da suka shafi yin ƙarya a takardun mallakarsu, da rashin cikakkun takardu, da rashin samun takardar izini daga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasar NAFDAC, da kuma sauran laifuka.

Babban jami'in ya ce hukumar tasa ta kama kwantenonin ne cikin wata uku da suka gabata.

Ya kuma tabbatar wa 'yan ƙasar cewa rundunarsu da ke aiki a Rivers ƙarƙashin za ta ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da kare lafiya da hana shigar da kayayyaki cikin ƙasar ta ɓarauniyar hanya.

Post a Comment

0 Comments