Shugaban jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, Farfesa Rufa'i Alƙali, ya ajiye muƙaminsa.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa sakataren jam'iyyar na ƙasa, kuma ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Farfesa Alƙali ya ce ya ajiye muƙamin nasa ne don bai wa sabbin jini dama, ta yadda za su ɗora a kan ci gaban da jam'iyyar ta samu cikin ɗan taƙaitaccen lokacin da ya yi yana jagorantar ta.Alƙali ya ce la'akari da irin abubuwan da suka faru kafin zaɓukan da suka gabata, da kuma a lokacin zaɓukan, yana cike da fatan cewa jam'iyyar adawar, na da makoma mai kyau.
Kuma a cewarsa, yana cike da fatan NNPP za ta kasance cikin manyan jam'iyyun siyasar ƙasar, da za su iya cin zaɓen shugaban ƙasa da sauran muƙamai a kakar zaɓe ta 2027.
Ya ƙara da cewa don cimma wannan buri, NNPP na buƙatar yin tunani da kuma kyakkyawan shiri, abubuwan da yanzu ne lokaci mafi dacewa na yin su.
Farfesa Rufa'i Alƙali ya kuma ce jam'iyyar na buƙatar sauye-sauye da dama, ta fuskar shugabancinta a matakai daban-daban domin ƙara ƙarfafa matsayinta.
Na kuma gamsu cewa wannan sauyi dole ya fara ta kaina. wannan shi ne dalilin da ya sa na ajiye muƙamina, don ba da dama ga sabbin hannu su ɗora daga inda muka tsaya game da gudunmawar da muka bai wa NNPP'', in ji Alkali.
Ya kuma miƙa saƙon godiya ga jagoran jam'iyyar na ƙasa Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso da ɗaukacin mambobin kwamitin amintattu na NNPP, da sauran zaɓaɓɓun 'yan siyasa na jam'iyyar bisa damar da ya ce sun ba shi wajen gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali.

0 Comments