Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta kama wani mutum da ake zarginsa da yiwa wata jaririya ‘yar wata 9 da haihuwa fyade a jihar Legas.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP. Benjamin Hundeyin ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Laraba.
Ya ce, tun farko wani mutum ne ya kai wa ’yan sanda korafin cewa wani matashi É—an shekara 27, ya yiwa wata jaririya fyade.
Ya ce mutumin ya kai korafin ne da misalin karfe 10:00 na daren Litinin.
Benjamin ya kuma ce, wanda ake zargin ya shiga gidan mahaifiyar jaririyar inda ya sameta a kwance ita kaÉ—ai, saboda uwar ta fita waje yin sayayya.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Legas, ya ce, anan ne wanda ake zargin, ya yi wa jaririyar fyade sannan ya ranta a na kare.
Sai dai wajen misalin karfe 11:00 na daren Talata, jami’anmu da ke ofishin Ijora Badiya sun cafko shi a inda yake buya.
Sai dai wajen misalin karfe 11:00 na daren Talata, jami’anmu da ke ofishin Ijora Badiya sun cafko shi a inda yake buya.
Benjamin ya kuma ce da wacce take karar da wanda ake zargin sun bayar da bayansu, inda ta ce wanda ake zargin ya amsa laifin lokacin da ake yi masa tambayoyi.
Jaridar1hausa247news


0 Comments